A wasan Bundesliga da muke kawo muku kai tsaye, wannan makon mun zabo muku kulob din FC Köln wato Kolon da kuma Hoffenheim. Inda Abdourrahmane Hassane da Yusuf Bala za su kawo muku shirin. Sai ku kasance da mu ranar Asabar kai tsaye daga karfe uku da mintuna 25 na rana agogon Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, karfe biyu da mintuna 25 na rana ke nan agogon GMT da Ghana. Za a iya sauraron yadda ta ke kayawa a wasan kai tsaye ko dai ta rediyo ko kuma ta shafinmu na intanet.
Thulisile Madonsela jaruma kan aikinta, ita dai Madonsela ta yi fice a duniya lokacin da ta rike mukamin babbar mai gabatar da kara na kasar Afirka ta Kudu, inda ta bankado wawurar dukiyar kasa wanda shugaba Jacob Zuma ya yi


Shugaban Najeriya ya ce muddin ba a ba wa 'yan gudun hijira kulawa da ta dace ba za a bude musu kofar tada kayar baya.
A cikin shirinmu na yammacin yau, jigon rahotannin zai maida hankali kan zaben kasar Ghana mako guda kafin a yi shi. Sai kuma Rikicin da ya barke a kudancin Kaduna, muna dauke da rahoto kan halin da ake ciki a birnin Maiduguri bayan da kwanakinnan aka fara ganin dawowar hare-haren ta'addanci. Ita kuwa Hukumar Lafia ta Duniya WHO, ta bullo da sabbin dabarun gwajin cutar HIV cikin sirri, muna dauke da labarin wasanni kan wasan kwallon kafan matan Afirka da ke gasa yanzu haka a kasar Kamaru.
Shirye-shirye kuwa akwai Taba ka lashe sai shirin Mutum da duniyarsa
Cikin shirin rana da yanzunnan ke zuwa muku, akwai batun musantawa da gwamnan Borno Kashim Shettima ya yi na alkaluman wadanda rikcin Boko Haram ya shafa. Muna kuma dauke da rahoto kan gargadin shugaba Buhari na cewa in ba'a kula da 'yan gudun hijiraba to suma za su tsama yan Boko Haram. Sai halin da ake ciki a rikicin Jamuhriyar Afirka ta Tsakiya, kana da rahoto bisa ayyukan kafafen yada labarai a Nijar.
Muna dauke da shirin sauyi a Afirka da kuma Ra'ayin matasa
DW - Hausa updated their cover photo.
A ranakun Asabar sashen Hausa na DW zai rika kawowa mai sauraro wasan kwallon kafa na Bundesliga da ake yi a nan Jamus kai tsaye daga karfe uku da mintuna 25 na rana agogon Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, karfe biyu da mintuna 25 na rana ke nan agogon GMT da Ghana. Za a iya sauraron yadda ta ke kayawa a wasan kai tsaye ko dai ta rediyo ko kuma ta shafinmu na intanet wato dw.com/hausa
Ta ya kuke ganin za a kawo karshen irin wadannan hare-hare a duniya baki daya?
Sakamakon irin rikicin siyasada ma kungiyoyin farar hula da ake samu a Janhuriyar Nijar, ya sa aka kira taron na wannan Talata. Shin mene ne tasirin irin wannan yunkuri na kungiyoyin kasashen waje kamar Amurka, wajen warware matsalar musamman ta cikin gida?
Shirin Ra’ayin Matasa na wannan makon, ranar Laraba 30.11.2016, zai maida hankali ne, a kan wani taro, da wata kungiyar kasa-da-kasa, ta hada, wanda ya hada matasa, daga wasu kasashen yammacin Afirka, kamar su: Najeriya, Nijar, Kamaru, Chadi, da Mali, domin ganawa a Maiduguri, jihar Borno, da ke Najeriya, da nufin samun musayar ra’ayoyi, a yayin da suke tattaunawa, kan batun matsalar rashin tsaro, da hanyoyin warwareta, da kuma magance karuwar masu tsattsaurar ra’ayi, da kuma dakile shigewa, kungiyoyin gwagwarmaya.
Ko, shin mene ne ra’ayoyin matasa, masu sauraronmu, a kan wannan yunkurin, na matasan yammacin afirka?
Muna sauraron ra’ayoyinku matasan afirka…….
Barkanmu da wannan yammaci. Da misalin karfe 7 agogon Najeriya da Kamaru da Chadi Zulaiha Abubakar Kibiya za ta gabatar muku da shirinmu na dare.
Inda za ku ji cewar, an gudanar da taron jam'iyyun siyasa da kungiyoyin farar hula a Janhuriyar Nijar da nufin warware rigingimu.
A Ghana kuwa, al'ummar kasarce ke neman 'yan siyasa su sayi kuri'unsu, ganin cewar ba wanda ake zaba ya ke cin zaben ba.
...A Najeriya kuwa taro ne aka gudanar dangane da lalubo hanyar kawo karshen aurar da yara mata tun suna kanana.
Za mu leka kasar Afirka ta kudu domin jin yadda ta kaya tsakanin shugaba Zuma da jam'iyyarsa ta ANC bayan ya tsallake kuri'ar yankan kauna a majalisar kasar.
Shirin zai duba halin da ake ciki, a cigaba da hare haren da ake kaiwa a birnin Aleppon kasar Siriya.
Ku kasance da shafukanmu na sada zumunta na Facebook da Twitter don samun labatu da dumi duminsu.
Barkanmu da war haka. Nan gaba kadan da misalin karfe 2 agogon Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, Zulaiha Abubakar Kibiya za ta gabatar muku da shirinmu na rana. Shirin da zai kunshi:
Yadda wasu al'ummomin jihar Bauchi suka ki amincewa allurar riga-kafin cutar shan inna, wanda ke zama koma baya ga yunkurin gwamnatin Tarayyar Najeriya na shawo kan cutar.
A Nijar kuwa kamfanonin garin Arlit ne suka gudanar da taron yini biyu kan makomar muhalli bayan sun kare ayyukansu.
...Muhawara ta barke a kasar Senegal dangane da sake farfado da hukuncin kisa shekaru 26 bayan soketa.
Masana kimiyyar ayyukan gona a Zimbabwe sun jaddada samar da sabbin irin shuka na Masara masu jure wa fari domin bunkasa abinci da kawar da yunwa.
Za ku iya samun labaru da dumi-duminsu ta shafukanmu na sada zumunta na Facebook da Twitter.
Shugabar Koriya ta Kudu ta mika kai ga majalisar dokoki ta dau mataki kan makomarta bayan kira ta sauka daga mulki.
Masu sauraro a cikin shirin Yamma da Salissou Boukari zai jagoranta za aji cewa bangaren sadarwa yana taka muhimmayar rawa a tattalin arzikin Naheriya.
Sannan matasa suna taro a birnin Maiduguri na Najeriya domin kan dakile tashe-tashen hankula masu nasaba da matsananci ra'ayi.
Kana majalisar dokokin dokokin Jamhuriyar Nijar ta yi muhawara kan diokar da ta hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
...A kasar Kamaru yankuna masu magana da harshen Ingishi sun yi watsi da kira kan janye yajin aiki.
A kasar Yuganda an fafata tsakanin jami'an tsaro da wasu tsageru dauke da makamai, abin da ya janyo mutuwar mutane 55.
Rahoto na musamman dangane da yunkurin matsa na tafiya ci-rani a kasashen Larabawa da Turai. Cikin Rahoton zaku ji matashi dan Kano da ya yi yunkurin zuwa Turai amma tun tafiyar bata yi nisa ba ya fasa. Ko menene dalilinsa? Za kuji a cikin wannan rahoton.
Ma'abota shirye-shiryen sashen Hausa na DW barkanmu da sake kasancewa tare da ku a wata sabuwar muhawara a shafinmu na sada zumunta na Facebook kan jerin rahotannin na musamman da muke kawo muku a kan kokarin dakile kwararar bakin haure zuwa Turai mai taken "Hangen Dala......Muna dakon ra'ayinku a cikin muhawarar tamu ta yanzu kan matsalar tafiyar matasan kasashen Afirka ciki kuwa har da Najeriya duk kuwa da irin dinbin tattalin arzikin da Allah Ya huwacewa wannan kasa. Marabanku
























